in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi zai halarci bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao na 2018
2018-04-03 13:59:16 cri
Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya sanar a gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta gudanar a ranar 3 ga wata cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin bude taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao na shekarar 2018, kuma zai gabatar da jawabi, zai kuma gana da shugabanni da kusoshin gwamnatoci na kasashe masu halartar taron da shugabannin hukumomin duniya, da 'yan majalisar dandalin, da yin tattaunawa tare da wakilan 'yan kungiyoyin 'yan kasuwa na kasar Sin da na kasashen waje. Wannan ne karo na uku da shugaba Xi Jinping zai halarci taron shekara-shekara na dandalin tattaunawar a matsayin shugaban kasar Sin, wannan ya shaida cewa, shugaba Xi Jinping da gwamnatin kasar Sin sun dora muhimmanci sosai da nuna goyon baya ga dandalin tattaunawar.

Shugaban kasar Austria Alexander van der Bellen, da shugaban kasar Philippines Rodrigo Duterte, da firaministan kasar Mongolia Ukhnaagiin Khürelsükh, da firaministan kasar Netherlands Mark Rutte, da firaministan kasar Pakistan Shahid Khaqan Abbasi, da firaministan kasar Singapore Lee Hsien Loong, da kuma babban sakataren MDD Antonio Guterres, da shugabar asusun ba da lamuni ta duniya Christine Lagarde su ma za su halarci taron. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China