Kasancewar a bana ake cika shekaru 40, tun bayan fara daukar manufar bude kofa ga kasashen waje da gyare-gyare a kasar Sin, lamarin da ya sanya shugaba Xi yin bayani kan yadda kasar Sin za ta kara bude kofa, da zurfafa gyare-gyaren da take yi. Haka zalika, shugaban ya bayyana matsayin da kasar Sin ta dauka a fannonin yunkurin samar da kyakkyawar makoma ta bai daya ga daukacin al'ummomin nahiyar Asiya da na duniya baki daya. (Bello Wang)