Fannonin da za'a zuba jarin sun kunshi ayyukan samar da muhimman kayayyakin more rayuwa da suka hada da fadada filin jirgin sama na Urumqi, da gina manyan titunan mota, da layukan dogo a yankin.
Aikin zai kuma kunshi gina wuraren adana ruwa da kula da albarkatun ruwan, kana da samar da layukan lantarki.
A shekarar 2017, yankin na Xinjiang ya zuba jarin kimanin yuan biliyan 450 wajen ayyukan gina kayayyakin more rayuwa, inda aka samu karin kashi 50 bisa 100 a wannan shekara. (Ahmad Fagam)