in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Xinjiang na shirye shiryen bikin babbar sallah
2017-08-31 20:31:44 cri
Gobe Jumma'a ce ranar babbar sallah ga al'ummar musulman duniya, domin share fagen zuwan ranar bikin sallah, al'ummar jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta Uygur da ke arewa maso yammacin kasar Sin, na shiga kasuwanni don sayen dabbobin layya da kayan lambu da 'ya'yan itatuwa, da ma sauran kayayyaki na bukata.

Domin biyan bukatun al'umma, tun daga satin da ya gabata, an kara yawan naman da ake adanawa ga al'umma a sassa daban daban na jihar. A kasuwanni kuwa, an cika shaguna da ganyaye da 'ya'yan itatuwa domin bukatar masu sayayya.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China