in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bukaci kasashen Afrika su mai da ayyukan noma jigo wajen samun ci gaba
2017-07-25 09:00:46 cri

Tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo, ya ce akwai bukatar kasashen Afrika su dauki matakin sake fasalin harkokin noma domin mayar da shi jigo wajen samun ci gaba.

Olusegun Obasanjo, ya yi kiran ne lokacin da yake jawabi yayin bikin cika shekaru 50 na cibiyar kula da harkokin noma a kasashe masu zafi ta kasa da kasa wato IITA a birnin Ibadan na jihar Oyo dake kudu maso yammacin kasar.

Tsohon shugaban kasar ya ce, har yanzu, kudin da ake kashewa na shigar da kayayyakin abinci cikin nahiyar na da matukar yawa, inda ya kai kusan dala biliyan 35 a kowace shekara.

Ya kara da cewa, an yi hasashen bukatar abinci zai kara karuwa da kusan kashi 20 bisa dari cikin shekaru 15 masu zuwa a fadin duniya, inda ake sa ran bukatar za ta fi yawa a nahiyar Afrika da gabashin Asiya, yana mai cewa, idan ba a dauki mataki ba, kudin da ake kashewa na shigar da kayayyakin abinci nahiyar Afrika zai kara karuwa.

Har ila yau, Obasanjo ya ce, za a iya fattakar yunwa baki daya idan shugabannin Afrika za su yi amfani da alfanun dake akwai a fannonin fasaha da kirkire-kirkire da bincike.

Ya ce, ba za a iya cimma wannan manufa ba, har sai dukkan bangarorin da batun ya shafa da masu ruwa da tsaki sun ba bangaren harkokin noma kulawar da yake bukata.

Tsohon shugaban kasar ya yi kira da a kawar da matsalar yunwa a Afrika ta hanyar zuba jari don samar da kayayyakin more rayuwa da gudanar da bincike da kuma samar da ci gaba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China