in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta fara fitar da albarkatun gona zuwa kasashen waje
2017-06-30 09:43:23 cri

Ministan aikin gona da raya karkara na Nijeriya Audu Ogbeh, ya ce gwamnatin kasar na gab da samun gagarumar nasara a yunkurinta na sake fara fitar da albarkatun gona zuwa kasashen waje.

Audu Ogbeh ya bayyana haka ne jiya a Lagos, cibiyar tattalin arzikin kasar, yayin kaddamar da shirin fitar da doya da kwamitin kwararru kan fitar da doyar Nijeriya da ma'aikatar aikin gona da raya karkara ta kasar suka shirya.

Ministan ya bukaci masu fitar da albarkatun gonar su tabbatar da cewa, kayayyakin da za su fitar sun cika ka'idoji da ingancin da kasashen ketare ke bukata, yana mai cewa, gwamnati ba za ta lamunci wulakanci ba idan aka ki karbar doyar kasar a Birtaniya da Amurka.

Audu Ogbeh ya ce, ana sa ran nasarar shirin na fitar da doya zai kara samar da kudin shiga da kyautata rayuwar al'umma tare da samar da aikin yi.

Ya kara da cewa, shirin zai ba mata da matasa damar shiga a dama da su a cikin harkokin gona ta hanyar samar da shirye-shiryen sana'o'i masu dorewa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China