Wata sanarwa daga kungiyar hadin kan Afirka ta AU, ta bayyana shirin kungiyar na fidda wani bayani, na awon nasarar da nahiyar ke samu a fannin ci gaban noma wanda aka yiwa lakabi da AATS.
Ana dai sa ran kaddamar da bayanin ne yayin taron shugabannin kungiyar na 30 dake tafe a ranar 28 ga watan nan da muke ciki. AATS zai zamo bayani irin sa na farko da kungiyar za ta gabatar, wanda zai kunshi sakamakon ci gaban noma da aka tattara daga sassan nahiyar daban daban.
Kaza lika kungiyar za ta fitar da rahoton ta na shekaru biyu biyu game da yadda ake aiwatar da yarjejeniyar Malabo ta watan Yunin shekarar 2014, game da ci gaban da najiyar ke samu a fannin dabarun gaggauta ci gaban ayyukan gona, da kyautata zamantakewa da rayuwar al'ummun nahiyar.(Saminu Alhassan)