Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya Ike Ekweremadu ya bayyana cewa, majalisar dattawan kasar ta kada kuri'ar da za ta kawo karshen hana shigo da man-ja da ma dangin kayayyakin da ake samarwa daga gare shi cikin kasar.
Ekweremadu wanda ya bayyana hakan a jiya Talata, ya ce majalisar ta dauki wannan mataki ne don ceto sashen da ma manoma cikin gida, da kuma yadda za a bunkasa da kiyaye yadda ake samar da man-ja a cikin kasar.
Bugu da kari, wannan mataki zai taimakawa wajen farfado da bangaren samar da man-jan, ya kuma sanya shi bisa turbar da ta dace ta yadda zai taka rawar da ta dace a matsayin daya daga sassan dake samarwa kasar kudaden shiga, baya da samar da guraben ayyukan yi ga 'yan kasa.(Ibrahim)