in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kudu ta kaddamar da shirin bunkasa zuba jari a fannin ayyukan noma
2017-06-28 10:14:36 cri

Gwamnatin Afirka ta kudu ta kaddamar da wani sabon shiri da aka yiwa lakabi da APSS, wanda zai ba da damar bunkasa zuba jari, da cin gajiya daga ayyukan noma. Sabon shirin dai zai lashe kudin kasar Rand Biliyan daya, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 78.

Da yake kaddamar da shiri yayin taron baje kolin harkokin cinikayya da ya gudana a birnin Johannesburg, ministan ma'aikatar cinikayya da masana'antun kasar Rob Davies, ya ce shirin zai samar da zarafi na bunkasa zuba jari a hada hadar samar da karin hatsi da kayan lambu, tun daga gonaki zuwa wuraren sarrafa albarkatun gona.

Kaza lika zai fadada samar da kayayyakin more rayuwa da ake bukata, wajen samarwa, da sarrafa albarkatun gona, wanda hakan zai ba da dama ta cin karin gajiya daga harkar noma a kasar.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China