A 'yan kwanakin nan, akwai wasu shugabannin kasashe da na kungiyoyin duniya, wadanda suka zo nan kasar Sin don halartar taron shekara-shekara na dandalin tattaunawa tsakanin kasashen Asiya na Bo'ao, ciki har da shugabannin Austria, da Holland, da Singapore, tare kuma da babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya. Yayin da suke gudanar da shawarwari tare da takwarorinsu na kasar Sin, sun nuna cewa, ya kamata a kiyaye tsarin gudanar da cinikayya cikin 'yanci, da kara kawar da shinge, da samar da sauki ga harkokin zuba jari da cinikayya.
Game da wannan batu, Geng Shuang ya ce, matakan da kasar Amurka ke dauka, musamman na kara sanya haraji kan hajjojin da kasar take shigarwa daga kasar Sin, matakai ne na bada kariya ga harkokin cinikayya, wadanda ba ma kawai ke yin illa ga moriyar kasar Sin ba, har ma na iya yin mummunan tasiri ga moriyar sauran kasashe.
Ra'ayoyin da wasu shugabannin kasashen duniya gami da na kungiyoyin kasa da kasa ke da su, sun shaida cewa, kasa da kasa sun amince cewa, ya zama dole a girmama dokoki gami da ka'idojin kasa da kasa, kana, kuskuren da Amurka ta aikata, ya riga ya janyo damuwa matuka ga kasashen duniya da dama.(Murtala Zhang)