in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na son kara bunkasa hulda da Amurka, in ji ministan harkokin wajen kasar
2016-11-14 10:23:00 cri
Ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi, ya gana da mamema labarai a jiya Lahadi tare da takwaransa na kasar Turkiyya Mevlut Cavusoglu, bayan da suka yi shawarwari a birnin Ankara.

A yayin da yake amsa tambaya game da ko kasar Sin na tuntubar zababben shugaban kasar Amurka Donald Trump da tawagarsa, Mr. Wang Yi ya ce, kasar Sin na fatan ci gaba da hadin gwiwa da gwamnatin Obama, don tabbatar da bunkasuwar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka har zuwa lokacin kafuwar sabuwar gwamnati. Baya ga haka, kasar Sin na da burin tuntubar tawagar Trump, don kara fahimtar juna da kuma hadin gwiwa.

Kamar yadda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a cikin sakon taya murna da ya aike ga Mr. Trump, kasar Sin na son kara bunkasa huldar da ke tsakaninta da Amurka kan wannan sabon mafari, bisa manufar kaucewa arangama da juna, da girmama juna, da kuma cimma moriyar hadin gwiwa da juna, abin da yake nuni ga burin Sin na bin sabuwar hanyar inganta makomar huldar da ke tsakanin kasashen biyu.(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China