in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta shata layi a yakin cinikayya dake tunkarowa in ji ma'aikatar harkokin waje
2018-03-23 18:10:35 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta ce Sin ta daura damarar tunkarar duk wani yaki na cinikayya da Amurka ke neman haddasawa. Da take tsokaci game da wannan batu yayin taron manema labarai na rana rana da aka saba gudanarwa, mai magana da yawun ma'aikatar Hua Chunying, ta ce Sin na fatan Amurka za ta lura matuka da matakan da take dauka, domin kaucewa tafka kuskure.

Duk dai da irin kiraye kiraye da sassan 'yan kasuwa, da kungiyoyi tare da kwararru suka ta yi, a ranar Alhamis shugaban Amurka Donald Trump, ya sanya hannu kan wata takardar amincewa da kakabawa hajojin kasar Sin da suka kai dala biliyan 60 dake shiga Amurka haraji, tare kuma da wasu takunkumi da zai shafi jarin da Sin din ke zubawa a kasarsa.

A daya bangaren kuma, mashawarci ga fadar White House game da harkokin cinikayya ya shaidawa manema labarai cewa, kasar Sin za ta fuskanci matsala idan har ta ce za ta dauki fansa kan wadannan matakai na Amurka.

Game da hakan, Madam Hua ta ce wadannan kalamai na jami'in Amurkar kuskure ne, sun kuma nuna irin rashin fahimtar sa ga niyyar kasar Sin da karfinta na kare moriyarta ta halal. Kaza lika jami'in bai hango irin illar da Amurkar za ta fuskanta a sakamakon yadda ta kare aniyarta wajen daukar matakan ba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China