in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na adawa ga duk wani mataki da zai lahanta moriyar ta bisa hujjar zirga-zirgar jiragen ruwa cikin 'yanci
2016-04-29 10:29:09 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Madam Hua Chunying, ta bayyana cewa a ko da yaushe, Sin na girmama tare da goyon bayan sha'anin zirga-zirgar jiragen ruwa cikin 'yanci bisa dokokin kasa da kasa, sai dai kuma tana adawa ga duk wani mataki da zai lahanta moriyar ta bisa wannan hujja.

A gun taron manema labaru da aka saba gudanarwa, Madam Hua ta amsa tambayoyin manema labaru, game da tsokacin wasu 'yan majalisar dokokin Amurka, inda suka bayyana halascin Amurka ta rika tura jiragen ruwan ta zuwa sassan tekun kudancin kasar Sin cikin 'yanci.

Ya zuwa yanzu cikin ko wadanne watanni uku-uku Amurka na tura jiragen ruwan ta zuwa yankin, mataki da bai nuna wata babbar barazana ga kasar Sin ba, a cewar wasu 'yan majalisar dokokin kasar Amurka.

Dangane da batun, Madam Hua ta ce, Sin ta yi la'akari da wadannan bayanai, kuma ta lura da cewa, kafofin yada labaru na Amurka na nuna cewa, sojojin Amurka na yada jita-jita game da Sin, cewa tana haifar da babbar barazana ga yankin tekun kudancin Sin. Alal misali, a kwanan baya, mujallar The National Interest ta Amurka, ta bayyana cewa Amurkan ta damu, cewa wai Sin na haifar da barazana ga cinikin kasa da kasa bisa takadamar da ake samu tsakaninta da wasu kasashe kan ikon mallakar wasu yakunan dake teku na kudu na kasar Sin.

Mujallar ta ce wannan manufa ba ta da tushe, kuma a cewarta, sojojin Amurka sun tura manyan jiragen ruwa masu saukar jiragen sama zuwa tekun kudancin Sin don nuna karfinsu, inda darajar jiragen ruwan ta kai dalar Amurka biliyan 13. Kana a ko wace rana, ana bukatar kudi dalar Amurka miliyan 6.5 wajen tafiyar da wadannan jiragen ruwa, yayin da yawan bashin da ake bin Amurka a yanzu ya kai dalar Amurka trillian 1.9, don haka ba a sani ba ko wannan shirin da wasu tsirarrun jami'an ta ke goyon bayansa na zirga-zirgar jiragen ruwa cikin 'yanci ya samu goyon baya daga masu biyan haraji a kasar ta Amurka,In ji kakakin ma'aikatar wajen kasar Sin. (Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China