Abu na farko, ya kamata mu zurfafa daidaita sabane sabane dake tsakanin kasashen biyu yadda ya kamata, da tabbatar da wani wucin gadi mai armashi domin dangantakar tattalin arziki da kasuwanci tsakanin Sin da Amurka a yayin shigowar sabuwar gwamnatin Amurka, in ji mataimakin faraministan kasar Sin Wang Yang a yayin bude zaman taro karo na 27 na kwamitin hadin gwiwa na Sin da Amurka kan tattalin arziki da musanya (JCCT). Wannan ita ce tattaunawar tattalin arziki ta manyan jami'ai ta karshe tsakanin kasashen biyu a karkashin gwamnatin Barack Obama.
Abu na biyu, bangarorin biyu zasu fafada fannonin dangantakarsu, da samar da karin sakamako na hakika a fannin zuba jari tare, da tattalin arziki da fasahohin zamani da tsaron abinci.
Abu na uku, mataimakin faraministan Sin yayi kira ga bangarorin biyu da su mayar da JCCT wajen samar da karin kayayyaki da moriya, da kuma kara bunkasa matsayinta a cikin dangantakar tattalin arziki dake tsakanin kasashen biyu.
Sakataren kasuwancin Amurka, Penny Pritzker, ya nuna cewa JCCT ya maida kokarinsa kan bangarori mafi dacewa domin dangantaka, lamarin da ya bada dama wajen bunkasa kasuwanci da musanya tsakanin kasashen biyu a tsawon shekaru uku na baya bayan nan. (Maman Ada)