A cikin sakon, Xi Jinping ya bayyana cewa, ana sada zumunta a tsakanin Sin da Masar a dogon lokaci. A shekarun baya baya nan, Xi da shugaba al-Sisi sun kiyaye mu'amala da juna, da kara yin imani da juna a fannin siyasa, da inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da kara yin mu'amalar al'adu da juna, ta haka jama'ar kasashen biyu suna sada zumunta sosai, shugaba Xi yana matukar farin ciki da ganin hakan. Yana fatan kasar Masar za ta kara samun babban ci gaba bisa hanyar dake dace da yanayin kasar a karkashin jagorancin shugaba al-Sisi. Kana ya dora muhimmanci sosai ga dangantakar dake tsakanin Sin da Masar, yana son yin kokari tare da shugaba al-Sisi wajen sa kaimi ga raya dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon mataki don amfanawa jama'arsu. (Zainab)