in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole ne mu tuna da jarumai tare da shugaban kasar Sin a yayin bikin sharar kaburbura na Qingming
2018-04-05 12:28:12 cri

 

Duk lokacin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya tabo maganar jarumai, da kuma wadanda suka sadaukar da rayukansu domin al'umma, ba ya iya boye abun da yake ji a zuciyarsa. A wurare masu yawa a nan kasar Sin, shugaba Xi Jinping ya sha gudanar da ziyara domin tunawa da wadanda suka sadaukar da rayukansu domin al'umma.

Yau Alhamis 5 ga wata, rana ce ta bikin sharar kaburbura na Qingming a nan kasar Sin. A kan maimaita kalamin shugaban kasar ta Sin domin tunawa da abubuwan da suka faru a tarihi, da kuma tunawa da jarumai da kuma wadanda suka sadaukar da rayukansu domin al'umma.

Ko mene ne dalilin da ya sa ya zama wajibi mu tuna, da kuma kare mutuncin jarumai, da kuma wadanda suka sadaukar da rayukan su domin al'umma?

A wurare da dama, shugaba Xi Jinping ya kan ce, al'umma sun gaza wajen cimma burin bunkasuwa, sai dai duk da haka suna tunawa da jarumai, kana kasa na iya gazawa wajen samun kyakkyawar makoma, amma tana tunawa da wadanda suka sadaukar da rayukan su domin al'umma. Ko wace al'umma da ta iya samun ci gaba, ta shahara ne sakamakon halayenta da ya sha bamban da na saura. Kishin kasa, shi ne ainihin halayen al'ummar Sinawa, a kalaman shugaba Xi Jinping na kasar Sin. (Tasallah Yuan)

1  2  3  4  5  6  7  8  
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China