in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Najeriya ya taya sabon shugaban Afirka ta kudu murna
2018-02-16 12:11:00 cri

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya taya sabon shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, murnar kasancewa sabon shugaban kasa, yana mai alkawarta ci gaba da hadin gwiwa da sabon shugaban wajen karfafa alakar kasashen biyu.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a jiya Alhamis, cikin wata sanarwa da ofishin sa ya fita. Sanarwar ta kara da cewa, shugaban Najeriyar ya yi na'am da yadda majalissar dokokin Afirka ta kudu ta zabi shugaba Ramaphosa don ya jagoranci kasar sa.

Har ila yau shugaban Najeriyar ya jinjinawa jagororin Afirka ta kudu, da dattakun da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ya nuna, na amincewa ya yi murabus daga mukamin sa, bayan shan matsin lamba daga jam'iyyar sa ta ANC.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China