Wannan sharhi ya bayyana cewa, game da wannan sauyi da bangaren Amurka ya yi ba zato ba tsammani, jama'a da masana wadanda suka kware a fannin ilmin tattalin arziki, da 'yan majalissun dokokin kasar na jihohi daban daban, sun nuna shakku kan matakan da Donald Trump ya dauka.
Sharhin ya ce matakan dai, baya ga rashin amincewa daga bangaren al'ummar Amurka, sun kuma hadu da adawa daga dukkanin sassan fadin duniya. Idan an kaddamar da yakin cinikayya, tabbas ba wanda zai ci nasara. Kuma yanzu haka bangaren Sin yana aiwatar da matakan mayar da martani kan matakan bisa shirinsa, kuma zai sa bangaren Amurka ya gane ma'anar "Gudun gara a fadawa zago". Kaza lika al'ummar Amurka ma za su gane wanda ya yi musu alkawarin samar da alheri, amma a maimakon haka ya sanya su tunkarar rasa guraben ayyukan yi. (Sanusi Chen)