Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ta ruwaito cewa, la'akari da matakin Amurka na kin shiga yarjejeniya bisa dokokin WTO, ya zama wajibi kasar Sin ta yi amfani da tsarin warware takkadamar domin kare muradu da hakkokinta.
Duk da adawar da kasashen duniya suka nuna, gwamnatin Amurka ta dauki matakin sanya harajin kaso 25 kan karafa da kuma kaso 10 kan kayayyakin gorar ruwa da ake shigar da su kasar daga kasashen ketare ciki har da kasar Sin.
A cewar sanarwar, Amurka ta sabawa dokar WTO ta tabbatar da daidaito yayin cinikayya tsakanin kasa da kasa, bisa sanya haraji kan wasu daga cikin kasashe mambobin kungiyar WTO ciki har da kasar Sin, yayin da ta ware wasu kasashe da yankuna. (Fa'iza Mustapha)