in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba wanda zai ci nasarar rikicin cinikayya, in ji ma'aikatar kasuwancin Sin
2018-04-04 18:20:04 cri
Game da rikicin cinikayya da ke gudana tsakanin kasashen Sin da Amurka, mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Wang Shouwen, ya bayyana yau a nan Beijing cewa, matsayin da kasar Sin ke dauka a kullum, shi ne lalubo kofar daidaita wannan batu ta hanyar gudanar da shawarwari, da tattaunawa a bude har abada.

Wang Shouwen ya ce idan bangaren Amurka yana son yin shawarwari, bangaren Sin zai shiga shawarwarin bisa ka'idojin zaman daidai wa daida, da mutunta juna, ta yadda za a kai ga kawar da matsalolin dake tsakaninsu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China