Wata sanarwar da ma'aikatar cinikayya ta kasar ta fitar a yau Laraba, ta ce hukumar kula da harajin kayayyakin da ake shigo da su ta majalisar gudanarwar kasar Sin, ta yanke shawarar kara haraji da kaso 25 cikin dari kan kayayyaki iri 106 karkashin wasu rukunoni 14.
An dauki matakin ne bayan gwamnatin Amurka ta gabatar da jerin wasu kayayyakin da kasar Sin ke shigarwa kasarta da darajarsu ta kai biliyan 50, wadanda za ta karawa haraji da kaso 25 cikin dari.
A cewar ma'aikatar, ranar fara aiwatar da sabon harajin zai dogara ne kan ranar da gwamnatin Amurka ta kakaba nata harajin kan kayayyakin kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)