in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta girmama bukatar da manomanta suke da ita ta kara haraji kan waken soya da take shigowa daga kasar Amurka
2018-04-04 18:57:03 cri
A yau Laraba, mataimakin ministan ma'aikatar kudi na kasar Sin Zhu Guangyao, ya bayyana a nan Beijing cewa, yawan waken soya da kasar Sin ta shigo da shi daga Amurka, ya kai kashi 62 cikin dari, bisa jimillar waken soyan da Amurka ke fitarwa. Sannan yawan waken soya da kasar Sin ta shigo daga kasar Amurka ya kai kashi 34.39 cikin dari, bisa jimillar waken soya da kasar Sin ta shigo da shi daga ketare a shekarar 2017.

Sakamakon haka, manoman kasar Sin wadanda suke noman waken soya sun kai kara cewa, kudin alawus da gwamnatin kasar Amurka take biyan manomanta, ya haifar da illa ga moriyar manoman kasar Sin. Sabo da haka, dole ne gwamnatin kasar Sin ta mutunta moriyar manomanta, tare da mutunta bukatun da kungiyar noman waken soya ta kasar Sin take da shi. Sabili da haka, waken soya ya shiga kayayyakin Amurka da bangaren Sin zai karawa haraji.

A waje daya, Mr. Zhu Guangyao ya bayyana cewa, har yanzu wannan mataki bai fara aiki ba. Bangarorin biyu sun gabatar da bukatunsu a kan tebur ne kawai, amma yanzu lokaci ne na shawarwari tsakanin bangarorin biyu, bisa sharadi daya, wato dole ne bangarorin biyu su mutunta juna. Jami'in ya ce bai kamata kowane bangare ya sanya wani sharadi na ba gaira ba dalili ba. Mr. Zhu Guangyao ya jaddada cewa, asalin dangantakar tattalin arziki dake tsakanin kasashen Sin da Amurka ta cimma moriyar juna da samun nasara tare ce. Kuma sharadin yin shawarwari cikin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Amurka shi ne mutunta juna, sannan sharadin tattaunawa tsakaninsu shi ne yin hakuri da juna. Kana bai dace wani daga cikinsu ya kafa sharadi ba gaira ba dalili ba. Kaza lika ya zama wajibi a yi shawarwari mafiya dacewa, bisa hakikanin halin da ake ciki, idan har ana fatan kawar da sabani dake wanzuwa a tsakaninsu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China