in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in MDD ya nuna juyayin mutuwar Madikizela-Mandela
2018-04-03 11:14:04 cri
Mai magana da yawun MDD ya ce babban magatakardan MDDr Antonio Guterres yayi alhinin mutuwar Winnie Madikizela-Mandela, tsohuwar matar marigayi Nelson Mandela kuma shugaban gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata.

Sakatare janar na MDDr ya mika sakon ta'aziyya ga al'ummar kasar Afrika ta kudu da kuma iyalan marigayiya Madikizela-Mandela.

Ita dai Madikizela-Mandela ta mutu ne a jiya Litinin a Johannesburg, kuma ta rasu tana da shekaru 81 a duniya. Ta rasu ne a daidai lokacin da take karkashin kulawar iyalanta bayan ta shafe tsawon lokaci tana fama da jinya, lamarin da yasa aka yi ta dawainiyar kaita asibiti don nema mata magani tun a farkon wannan shekarar, kamar yadda iyalanta suka tabbatar da hakan.

Madikizela-Mandela ta kasance daya daga cikin jigo wajen fafutukar yaki da wariyar launin fata.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China