Jami'in ya kara da cewa, a zamanin da ake ciki, sauyawar yanayi na kara tasiri kan zaman rayuwar jama'ar duniya, lamarin da ya shafi gajeren lokaci da kuma na dogon lokaci, saboda haka tilas ne a nemi hanyar da za a bi domin daidaita lamarin.
Mista Guterres ya kuma ambaci alkaluman da asusun ba da lamuni na IMF ya bayar, wadanda suka nuna cewa sauyawar yanayin duniya ya haddasa hasarar da ta kai fiye da dalar Amuka biliyan 320 a bara, kana ambaliyar ruwa da ta abku a bara ta shafi mutane miliyan 41 a kudancin Asiya, da wasu dubu 900 a nahiyar Afirka.(Bello Wang)