in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sakatare janar na MDD ya yi kira da a karfafa hadin-gwiwa don tinkarar kalubalen kiyaye zaman lafiya
2018-03-29 12:52:51 cri

Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce, ayyukan wanzar da zaman lafiya da MDD ke gudanarwa na fuskantar babban kalubale, abun da ya kamata a dauki matakai na bai daya wajen kara samar da tabbaci ga ayyukan.

A wajen muhawarar da kwamitin tsaron MDD ya shirya kan ayyukan kiyaye zaman lafiya a jiya, Guterres ya ce, ayyukan wanzar da zaman lafiya da MDD take gudanarwa na fuskantar karin hadarurra da abubuwa masu sarkakkiya. A bara, masu kiyaye zaman lafiya 59 sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai musu, adadin da ya karu da mutane 25 idan aka kwatanta da na shekarar 2016.

Antonio Guterres ya kara da cewa, ya kamata a mai da hankali kan manyan fannoni uku don daukar matakai na bai daya. Na farko, a sake kafa alkibla ga ayyukan shimfida zaman lafiya. Na biyu, kara bada tabbacin tsaro da karfi ga ayyukan. Na uku wato na karshe shi ne, kara tura nagartattun sojoji dake rike da makamai masu karfi don samar da karin goyon-baya ga ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Har wa yau, Guterres ya ce, ya na nan yana kokarin shawartar dukkanin abokan hadin-gwiwa da masu ruwa da tsaki don samar da goyon-baya ga ayyukan shimfida zaman lafiya na MDD.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China