An dai sanya hannu kan yarjejeniyar ne a Kigali, babban birnin kasar ta Rwandan, wanda Dieu Uwihanganye, karamin ministan sufurin kasar Rwanda, da Hadi Abubakar Sirika, karamin ministan sufuri jiragen saman Najeriya suka rattaba hannu a madadin gwamnatocin kasashen biyu.
Yarjejeniyar ta kunshi batun hadin gwiwa wajen samar da horo da musayar kwararru a fannin sufurin jiragen saman kasashen Rwanda da Najeriya.
Yarjejeniyar za ta kara sadarwa tsakanin kasashen biyu da kuma bunkasa harkokin cinikayya a tsakaninsu, in ji Uwihanganye, bayan da suka kammala sanya hannu kan yarjejeniyar.
Ya ce yarjejeniyar wani tsari ne na cude-ni-in-cude-ka wanda zai hada sassan kasashen biyu wadda ake sa ran zai taimaka wajen bunkasa harkokin hukumomi masu zaman kansu domin amfanawa ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummomin kasashen biyu.
A yanzu haka jirgin saman RwandAir ya tashi zuwa birnin Lagos domin tsara yadda za'a fara sufurin daga Rwanda zuwa Abuja a watan Mayun shekara ta 2018. (Ahmad Fagam)