Wasu tsageru sun kashe wasu mutanen kauye 32 a jihar Zamfara dake arewa maso yammacin Nijeriya.
Shugaban karamar hukumar Anka Mustapha Gado, wanda ya tabbatar da aukuwar al'amarin, ya ce an binne mutane 32 a ranar Alhamis, ciki har da wata mata da danta, wadanda suka mutu a wani asibiti dake birnin Gusau.
Mustapha Gado, ya ce har yanzu ana bincike don gano wasu gawawwakin a daji, sannan an kara tsaurara matakan tsaro a yankin, sai dai a cewarsa, dukkan al'ummar kauyen sun tsere saboda fargabar kada tsagerun su kuma komawa.
Majiyoyi daga hukumomin taro sun ce tsagerun sun kai hari kauyen Bawan Daji ne a ranar Talata da ta gabata, bayan wasu mutanen yankin sun gudanar da taro don tattauna matakan da za su dauka kan tsagerun a lokacin daminar bana.
Majiyar ta kara da cewa, tun da farko dai, tsagerun sun yi barazanar cewa babu wani aikin gona da zai gudana a yankin a bana. (Fa'iza Mustapha)