Mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo da ya halarci bikin kaddamar da aikin, ya ce wannan sabuwar tashar jiragen ruwa za ta haifar da karin moriya ga yankin ciniki cikin 'yanci na Lekki. Yayin da a nasa bangare, Rotimi Amaechi, ministan sufuri na kasar, ya ce wannan tasha za ta taimaka wajen tabbatar da matsayin Najeriya na cibiyar zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin da take ciki.(Bello Wang)