in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 15 sun mutu, 83 sun jikkata a harin Boko Haram a Najeriya
2018-04-03 09:28:48 cri
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane 15 kana wasu 83 kuma suka jikkata yayin musayar wuta tsakanin sojojin Najeriya da mayakan Boko Haram a arewacin Najeriyar.

Soja guda da farar hula daya na daga cikin wadanda suka mutu a yayin gumurzun wanda ya faru a cikin birnin Maiduguri dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, da yammacin ranar Lahadi, kamar yadda kakakin rundunar sojojin Najeriya ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Ragowar mutanen 13 da suka mutu mayakan kungiyar Boko Haram ne wadanda suka yi yunkurin kutsawa cikin birnin Maiduguri, babban birnin jahar Borno, inji kakakin sojojin, Onyema Nwachukwu.

Nwachukwu ya ce, mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram sun sha kaddamar da hare hare kan wasu kauyuka dake kusa da birnin Maiduguri bayan sun sha yunkurin shiga cikin birnin amma hakarsu bata cimma ruwa ba.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ma, mutane 13 ne suka mutu kana wasu da dama suka jikkata a wasu hare haren boma bomai da aka kaddamar a wannan birnin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China