Bisa takardar da kungiyar EU ta gabatar, an amince da shawarwarin ficewar Birtaniya daga kungiyar EU bisa aya ta 50 dake cikin yarjejeniyar Lisbon da kuma ka'idojin da kungiyar EU za ta bi a yayin shawarwarin. Kana takardar ta jaddada kiyaye kasuwa da matsayin kasashe membobin kungiyar a yayin shawarwarin da sauransu.
A ranar 29 ga watan Maris ne firaministar kasar Birtaniya Theresa May ta mikawa kungiyar EU wasika, inda ta sanar da fara shirin ficewar kasarta daga kungiyar EU. Kasar Birtaniya da kungiyar EU suna da shekaru biyu don kammala shawarwarin ficewar kasar daga kungiyar ta EU. (Zainab)