in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Najeriya ta yiwa jam'iyyar adawar kasar raddi game da 'yan matan da aka kubutar
2018-03-23 10:41:25 cri

Gwamnatin Najeriya ta zargi babbar jam'iyyar hamayyar kasar ta PDP da makancewa wajen kasa ganin alheran jam'iyyar mai mulkin kasar, bayan da PDPn ta nuna cewa batun sace 'yan matan Dapchi da sakinsu wani dodorido ne da gwamnati mai ci ta kitsa.

Ministan yada labaru da raya al'adun kasar, Lai Mohammed, ya bayyana cikin wata sanarwa da aka aikewa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya ce, wadannan kalamai da PDPn ta yi ya saba hankalin bil adama, kuma rashin tunani ne, da rashin kishin kasa da jam'iyyar ke nunawa a fili.

Ya ce, tun da dai kubutar da 'yan matan na Dapchi ya faru ne biyowa bayan shiga tsakanin da aminan kasashe da kuma kungiyoyin kasa da kasa masu kima suka yi, to batun sace 'yan mata da sakinsu zai kasance wani makircin da aka shirya ke nan, wanda wasu kasashen duniya suka sa hannu a ciki.

Mohammed ya ce, martanin da jam'iyyar ta PDP ta mayar ya nuna a fili irin bakar adawar da jam'iyyar ke da shi, musamman duba da irin gazawar da jam'iyyar ta PDP ta nuna a lokacin da take kan madafun iko, a lokacin da ta gaza ceto matan da aka sace a zamanin mulkinta.

Ministan ya ce abin takaici ne ga jam'iyyar PDP wadda ta gaza rike matsayinta na jam'iyya mai mulki, yanzu ga shi ta sake nuna gazawarta a matsayinta na jam'iyyar adawa, duba da irin kalaman rashin dattakun da take furtawa game da sakin 'yan matan na Dapchi, wanda ya kasance wani muhimmin abin farin ciki da ya kamata ko wane dan kasa na gari zai yi murna da shi ba tare da nuna adawa ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China