in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Assad ya gana da Putin a Syria
2017-12-11 20:14:04 cri
A yau ne, shugaban Syria Bashar al-Assad na Syria ya gana da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin a Syria.

Wannan shi ne karon farko da shugaba Putin ya ziyarci sansanin sojojin saman Rasha dake birnin Latakia na kasar Syria, tun lokacin da aka fara rikicin kasar Syria shekaru 6 da suka gabata.

Rahotanni na cewa, bayan ganawa da shugaba Assad, Putin kuma ya duba sojojin dake sansanin, inda ya umarci ministan tsaronsa da ya shirya janye sojojin Rashar dake kasar ta Syria.

Shugaba Putin ya ce, idan har 'yan ta'adda suka sake kunno kai, za su fuskanci martanin da ba su taba gani ba. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China