in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na goyon bayan MDD ta jagoranci shiga tsakani kan tattaunawar zaman lafiya a Syria
2017-11-29 09:42:55 cri
Manzon musamman na kasar Sin kan batun Syria Xie Xiaoyan, ya ce kasar Sin na goyon bayan MDD ta jagoranci shiga tsakani kan batun tattaunawar zaman lafiya a Syria tare da samar da tsarin siyasa a kasar da yaki ya daidaita.

Xie Xiaoyan, ya ce kasar Sin za ta mara baya ga duk wani yunkurin da zai taimaka wajen warware matsalolin, kuma a shirye take ta hada hannu da bangarorin da batun ya shafa, wadanda ke da karfin fada a ji a tattaunawar zaman lafiyar.

Wakilin na Sin ya gana a lokuta mabambanta da manzon musamman na MDD a Syria Staffan De Mistura da kuma takwarorinsa na kasashen Rasha da Amurka. Ya kuma halarci taron da MDD ta jagoranci shiryawa kan shirye-shirye gudanar da wani sabon zagayen tattaunawar neman zaman lafiya a Syria.

A nasa bangaren, Staffan De Mistura ya yaba da goyon bayan kasar Sin, yana mai cewa rashin nuna bangaranci da muhimmin matsaya da kasar Sin ta dauka, ya taka rawa gaya wajen samar da mafita a siyasance kan batun Syria, kuma a shirye yake ya ci gaba da tuntuba da hadin gwiwa da kasar Sin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China