in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta yi Allah wadai da manufar Amurka ta kafa rundunar dakarunsa kai a arewacin kasarta
2018-01-15 20:17:48 cri
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta fidda wata sanarwar dake Allah wadai da shirin kasar Amurka na kafa wata rundunar dakarun sa kai mai dauke da makamai a arewacin kasar, tana mai bayyana hakan da wani yunkuri na keta 'yancin kan kasar.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta kara da cewa, manufar Amurkar ta sabawa dokoki na kasa da kasa, baya ga keta hurumin kasar na cin gashin kai da wannan mataki zai haifar. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China