Mahukuntan birnin Beijing sun yi hasashen samun karin yawan kudaden da ake kashewa ta hada hadar cinikayya da ake yi a yanar gizo, inda aka yi hasashen cewa, ya zuwa karshen shekarar bana, adadin wadannan kudade na iya kaiwa kudin Sin Yuan tiriliyan 2.5.
Mahukuntan birnin na Beijing dai sun shirya kara kaimi ga inganta tsare tsaren amfani da fasahohin yanar gizo ko Intanet, matakin da zai samar da damar bunkasa hidimomin cinikayya ga masu saye da sayarwa dake amfani da kafar.
Har ila yau za a kara yayata damar ci gaban kamfanoni dake amfani da wannan kafa a sassan kwaryar birnin da ma yankunan karkakar sa. A hannu guda kuma za a karfafawa masu hada hadar cinikayya gwiwar mayar da sana'o'in su kan yanar gizo.
Bugu da kari, mahukuntan na Beijing za su tsara hanyoyin ba da horo, da na ka'idojin safarar kayayyakin da ake cinikayya ta yanar gizo, da kuma tsarin amfani da na'urorin sufuri, domin gabatarwa masu sayen kaya abubuwan da suka saya domin cimma wannan kuduri.(Saminu)