in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakin da Amurka ta dauka na kara harajin kwastam kan kayayyaki kirar kasar Sin, gazawa ce da kuma keta ka'idojin da bangarori da dama ke bi
2018-03-29 15:43:02 cri
A yau Alhamis, kakakin ma'aikatar kasuwancin kasar Sin Gao Feng ya bayyana cewa, shirin kasar Amurka na karbar karin harajin kwastam kan kayayyakin kirar kasar Sin da darajarsu za ta kai dalar Amurka biliyan 60, tamkar gazawa ne da kuma keta ka'idojin da bangaori da dama ke bi, mai yiyuwa ne zai haifar da karin matsalolin kariyar cinikayya. Sakamakon haka, tattalin arzikin dukkan kasashen duniya dake samun farfadowa sannu a hankali ya sake shiga wani yanayi na rashin tabbas. Kakakin ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ba ta son yakin cinikayya, amma ba ta fargabar duk wani abu da ya shafi wannan batu. Inda ya karfafa cewa, kasar Sin tana da imani sosai wajen tunkarar dukkan matakan kare cinikayya da ake dauka a fannonin cinikayya da zuba jari. Ya kuma bukaci bangaren Amurkar da ya dakatar da aiwatar da matakinsa ba tare da bata lokaci ba, idan ba zai yi hakan ba, ko shakka babu, kasar Sin za ta ci gaba da yin wannan yakin cinikayya.

Mr. Gao Feng ya kuma gargadi bangaren Amurka da ya guji daukar duk wani matakin da zai iya kawo illa ga dangantakar cinikayya dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Idan ba zai yi hakan ba, to makakin zai iya zama tamkar kaikayi ne koma kan mashekiya. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China