Ministan kula da harkokin cinikayya Zhong Shan, ya ce cikin shekaru 5 da suka gabata, kayakkin da ake amfani da su a kasar da cinikayya da kasashen ketare da harkokin zuba jari na kasar Sin, sun zarce na yawancin kasashen duniya, abun da ya shimfida tubali mai karfi na ci gaban tattalin arziki da cinikayya.
Bunkasar harkokin cinikayyar kasar Sin ya bada gudunmuwa ga farfado da cinikayya da tattalin arzikin duniya, inda mutane a fadin duniya ke amfana daga kayakkin da kasar Sin ta samar, yayin da kayayyakin da ake shigo da su kasar ke taimakawa wajen bunkasa cinikayyar abokan huldarta. (Fa'iza Mustapha)