Bikin baje kolin dai zai kasance karo na 6 da sassan za su gudanar. A kuma shekara mai zuwa zai gudana ne a birnin Urumqi, fadar mulkin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta.
Mashirya baje kolin dai sun bayyana cewa, fadin wurin da za a gudanar da baje kolin ya kai sikwaya mita 140,000. Zai kuma kunshi rumfunan masu zuba jari da masu hadin gwiwar cinikayya. Sai kuma fannin yaki da fatara, da dunbin kayayyakin sarrafawa na masana'antu, tare kuma da na dab'i. (Saminu Hassan)