in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Isra'ila ta jingine yarjejeniyar ta da MDD game da tsugunar da 'yan ci rani
2018-04-03 20:52:51 cri
Kasar Yahudawa ta Isra'ila ta jingine matsayar da ta cimma da MDD, game da baiwa wasu masu neman mafaka 'yan asalin Afirka matsuguni a yankunanta, kwana guda kacal da amincewa da hakan. A Talatar nan ne ofishin firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya fitar da wata sanarwar dake watsi da yarjejeniyar da sassan biyu suka cimma.

Da yammacin ranar Litinin ne dai kafafen talabijin suna nuna Mr. Benjamin Netanyahu, na bayani yayin wani taron manema labarai, inda ya bayyana amincewa da matsayar da kasarsa ta cimma tare da hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ta MDD.

Karkashin yarjejeniyar da a yanzu ta ci karo da koma baya, Isra'ila za ta tsugunar da wani bangare na adadin masu neman mafaka daga kasashen Eritrea da Sudan, inda kuma aka amince za a kwashe wasu daga cikinsu zuwa wasu kasashen yammacin Turai.

Sai dai kuma daga bisani Mr. Netanyahu ya rubuta a kan shafin sa na Facebook cewa, ya jingine wannan matsaya da a baya ya amince da ita.

Rahotanni sun bayyana cewa firaministan na Isra'ila ya fuskanci suka daga wasu ministocinsa, wadanda suka yi zargin cewa bai yi shawara da su ba kafin amincewa da waccan yarjejeniya, baya ga wasu kungiyoyi na masu rajin kishin kasa, da ke goyon bayan tusa keyar masu neman mafakar zuwa kasashen su na asali. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China