Tun da farko a daren Lahadi, an yi ta jin karar jiniya a wasu birane da dama dake kudancin Isra'ila, kuma kakakin rundunar sojan ya samar da cewa cibiyar kakkabo makaman rokar ta kakkabo rokoki da dama da aka harba daga zirin Gaza zuwa Isra'ila.
Daga bisani an gano cewa babu wasu makamai da aka harba a yankunan Yahudawan da kuma cibiyar kakkabo makaman rokar wadanda aka harba daga yankuna dake karkashin ikon Palastinawa.
Wannan bude wutar wani bangare ne na rawar dajin da dakarun sojojin kungiyar Hamas, kungiyar fafutukar Palastinawa mafi girma dake zirin Gaza ta gudanar. (Ahmad Fagam)