in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palesdinu ta yi kira ga MDD da ta tabbatar da yunkurin shimfida zaman lafiya a tsakaninta da Isra'ila
2018-02-19 12:58:46 cri
A jiya Lahadi 18 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Palesdinu Riyadal Malki, ya yi kira ga MDD da ta tabbatar da yunkurin shimfida zaman lafiya a tsakanin Palesdinun da Isra'ila bisa tushen shirin "Kafa kasashe biyu".

Malki ya bayar da sanarwa a wannan rana a birnin Ramallah dake yammacin gabar kogin Jordan cewa, bisa halayyar kasar Amurka ta nuna goyon baya ga Isra'ila, ya kamata kwamitin sulhu na MDD ya dauki matakai masu dacewa wajen aiwatar da kudurorin duniya dake shafar Palesdinu, da daukar alhaki ga jama'ar Palesdinu a fannin dokoki, da tabbatar da hakkinsu.

Sanarwar ta bayyana cewa, don warware batun nuna rashin adalci ga jama'ar Palesdinu, da hana Isra'ilan mamayar da take yi na gina matsugunan Yahudawa a yammacin kogin jordan, da amincewa Palesdinu a matsayin kasa mamban MDD a hukunce.

Ana saran cewa, kwamitin sulhun MDD zai gudanar da wani taro a ranar 20 ga wannan wata, inda shugaban al'ummar Palesdinu Mahmoud Abbas zai yi jawabi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China