Mataimakin shugaban Amurkan ya yi wannan furuci ne a lokacin da yake gabatar da jawabi gaban majalisar dokokin Isra'ila a jiya Litinin, abun da ya jawo zanga-zangar wasu kansiloli 'yan asalin kasashen Larabawa, inda suka daga kwallayen dake rubuta cewa, birnin Kudus shi ne fadar mulkin Palasdinu.
A daya hannun kuma, a jiya Litinin, shugaban al'ummar Palasdinawa Mahmoud Abbas ya yi shawarwari tare da ministocin harkokin wajen wasu kasashen kungiyar tarayyar Turai a birnin Brussels na kasar Belgium, inda ya bayyana fatansa na cewa, tarayyar Turai za ta kara taka rawar a-zo-a-gani a fannin shimfida zaman lafiya tsakanin Palasdinu da Isra'ila, inda kuma ya bukaci kasashen Turai su amince da kasancewar Palasdinu a matsayin kasa mai cin gashin kan ta.
Har wa yau, game da haramta bayar da tallafin kudade da Amurka ta yi ga ofishin MDD na tallafawa Palasdinawa 'yan gudun hijira a yankin Near East wato UNRWA a takaice a watan nan da muke ciki, Abbas ya yi kira ga tarayyar Turai da ta kara samar da goyon-baya.
Sa'annan a nata bangaren, babbar wakiliya a fannin harkokin diflomasiyya da manufofin tsaro a kungiyar tarayyar Turai Madam Federica Mogherini ta jaddada cewa, tarayyar Turai za ta tsaya kan shirin kasancewar kasashe biyu, da ci gaba da nuna goyon-baya da tallafawa Palasdinu. Ta kuma kara da cewa, EU na goyon-bayan sake farfado da shawarwarin shimfida zaman lafiya tsakanin Palasdinu da Isra'ila. (Murtala Zhang)