Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Namibiya wanda ke ziyara a kasar Sin, jiya Alhamis a nan birnin Beijing. Wannan shi ne karo na biyu da shugaba Xi ya gana da shugaban kasar Afirka a cikin mako guda da ya gabata, inda a ranar 22 ga wannan wata, ya gana da takwaransa na kasar Kamaru Paul Biya a nan Beijing.
Yayin ganawar tsakaninsa da shugaba Hage Geingob na Namibiya, Xi ya bayyana cewa, babbar moriyar kasar Sin da ta kasashen Afirka suna dogara ne da juna, a don haka ya kamata sassan biyu su yi kokari tare domin karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu.(Jamila)