Kana ya kuma yabawa kasar ta Sin, inda ya bayyana cewa kasar Sin amintacciyar kasa ce wanda za'a iya dogara da ita ta fuskar mu'amala.
Nkurunziza ya bayyana hakan ne a lokacin tattaunawa da kafafen yada labaran kasar Sin, ya ce babban abin da ya karfafa kyakkyawar dangantaka tsakanin Burundi da Sin shi ne, an gina hadin gwiwar kasashen biyu ne bisa mutunta juna, da girmama juna, da kuma cin moriyar juna.
A bisa wata kididdiga daga ofishin jakadancin kasar Sin a Burundin ta nuna cewa, jarin cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai dala miliyan 46 a shekarar 2015. Kasar Sin tana sayen kofee da ganyen shayi mai matukar yawa daga kasar Burundi, yayin da kasar Sin ke sayar da kayayyakin sadarwa, da tufafi, da na'ura mai kwakwalwa zuwa kasar ta Burundi. (Ahmad Fagam)