Yayin da yake zantawa da 'yan jaridun kasar Sin, Nkurunziza yana mai cewa, akwai wasu kafofin watsa labaran kasashen yammacin duniya wadanda ke amfani da rahotanninsu domin kawo cikas tsakanin wasu kasashe, da tunzura fitina ko haddasa kiyayya tsakanin kasashen duniya. Nkurunziza ya ce, wadannan kafofin watsa labarai ba za su cimma nasara ba, saboda yanzu kasar Sin babbar aminiyar hadin-gwiwar kasashen Afirka ne wadda ba za'a iya maye gurbinta ba.
Har wa yau, a madadin kasarsa wato Burundi, Nkurunziza ya godewa gwamnatin kasar Sin matuka saboda ta dade tana kokarin ganin an yi mata adalci a fadin duniya. (Murtala Zhang)