in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
"The City" na London yana son ba da taimakon raya sabon yankin Xiong'an na Sin
2018-04-01 13:08:14 cri
Kwanan bayan, magajin garin yankin "The City" na birnin London Charles Bowman, ya bayyana a birnin Beijing cewa, yankin na "The City" yana da fasahohi masu kyau wajen kafa birni mai hikima, kuma yana sa ran ba da gudummawa kan raya sabon yankin Xiong'an mai hikima na kasar Sin ba tare da gurbata muhalli ba.

A matsayin magajin garin "The City" na London na 690, kwanan baya, Mr. Bowman ya kai ziyara a wasu wuraren kasar Sin da suka hada da biranen Beijing, Shanghai, Shenzhen, HongKong da dai sauransu, inda ya zo ne tare da wata tawagar wakilan harkokin kasuwanci.

Haka kuma, ya bayyana cewa, a matsayin bangare na kafuwar "The City" na hada-hadar kudi a cikin birnin London, kamfanin Canary Wharf ya kulla wata yarjejeniyar hadin gwiwa da sabon yankin Xiong'an a watan Janairu na bana, inda aka sa ran za su yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a iya neman ci gaban yankin Xiong'an, kamar yadda aka yi a yankin na "The City" na London.

A sa'i daya kuma, ya ce, birnin London yana son samar da ilmi na musamman game da harkokin sha'anin kudi, ayyukan ba da hidima da dai makamantansu, wadanda ya koya cikin shekaru da dama da suka gabata ga kasar Sin, domin ba da gudummawa yadda ya kamata kan bunkasuwar biranen kasar Sin, har ma da biranen kasashen duniya baki daya.

Bugu da kari ya ce, mai iyuwa ne za a iya raya yankin Xiong'an zuwa yankin sha'anin kudi na zamani dake kan gaba cikin kasa da kasa, sabo da "The City" ya kware kan wannan fanni, shi ya sa, yana son ba da taimako ga yankin Xiong'an da kuma samar da fasahohinsa ga yankin a fannonin gina yankin, yin nazari, tattara kudade da kuma gina ababen more rayuwa da dai sauransu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China