Da sanyin safiyar yau Jumma'a ne aka harba taurarin dan Adam guda 2 daga cibiyar harba kumbo dake birnin Xichang na kasar Sin, wadanda suka kasance tauraro na 30 da 31 cikin tsarin taurarin dan Adam masu kula da harkar sufuri da zirga-zirgar jiragen ruwa na kasar Sin da ake wa lakabi "Beidou". Inda aka yi amfani roka samfurin CZ-3B kirar kasar Sin, wajen harba taurarin 2.
Bayan harba taurarin, sun kwashe sa'o'i fiye da 3 suna shawagi, kafin su shiga cikin kwangirin da ya kamata su bi. Daga bisani za a gudanar da wasu gwaje-gwaje a kan taurarin 2, don neman sanya su yin aiki tare da sauran taurarin dan Adam na tsarin Beidou, wadanda suka riga suka kasance a sararin samaniya tun da farko.
Ana shirin kammala ayyukan gwaji a karshen bana, ta yadda tsarin taurarin dan Adam mai kula da harkar sufuri na Beidou zai iya fara samar da hidimomi ga kasashe da yankuna da suka sanya hannu a shawarar "ziri daya da hanya daya" ta kasar Sin.(Bello Wang)