in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin wajen Sin: daukar matakin kare kasuwar gida tamkar rufe kofa ne
2018-03-31 12:49:09 cri
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma Ministan harkokin wajen kasar, mista Wang Yi, ya halarci wani taron tattauna harkokin masana'antu da cinikayya karkashin shirin hadin gwiwa tsakanin kasashen dake yankin kogin Mekong, wanda aka kira a birnin Hanoi, fadar mulkin kasar Vietnam.

Da yake gabatar da jawabi yayin taron, mista Wang Yi ya ce a bana ne ake cika shekaru 40 da fara gudanar da manufar gyare-gyare da bude kofa a kasar Sin. Kuma idan aka yi waiwaye can baya, za a gano cewa, dukkan ci gaba da nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya tattalin arzikinta, ta same su ne bisa dogaro da manufar gyare-gyare da bude kofa. A don haka, za a ci gaba da tsayawa kan wannan manufa don neman samun ci gaban tattalin arziki mai inganci. Ministan ya kara da cewa, manufar na cikin manyan ka'idojin kasar da ba za a taba canza su ba cikin kowanne yanayi da za a fuskanta. A cewarsa, wannan manufa ta na taimakawa wajen kare moriyar jama'ar kasar Sin, har ma da amfanawa sauran kasashe.

Wang Yi ya ce, manufar bude kofa ta shafi bangarori 2 dake hulda da juna. Sa'an nan, samun sabanin ra'ayi ko kuma rikici yayin da ake cinikayya tsakanin kasa da kasa, ba wani abu ne na ban mamaki ba, inda ya ce kamata ya yi a kara tattaunawa, da neman daidaita lamarin bisa dokoki.

Bugu da kari, ya bayyana matakin wasu kasashe na daukar ra'ayi na kashin kai, da neman kare kasuwannin gida, tamkar mai da agogon hannu baya, wanda ba shi da wani alfanu, inda ya ce maimakon haka wahala za su sha. Jami'in ya kara da cewa, kasar Sin na son raba damammakin da ta samu tare da sauran kasashe. Amma idan ana son daukar matakin kare kasuwannin gida, to, hakan tamkar rufe kofa ne, kuma tabbas za a sha wahala bisa daukar wannan mataki.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China