in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: zancen da aka yi game da hadin gwiwar Sin da Afirka ba daidai ba ne
2018-03-31 13:11:38 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya halarci wani taron manema labaru a nan birnin Beijing na kasar a jiya Jumma'a, inda ya mayar da martani ga zancen da wasu kafofin watsa labaru na yammacin duniya suka yi, dake nuna shakku kan yadda kasar Sin take tallafawa kasashen Afirka. A cewar mista Lu, suna kallon kasar Sin ne bisa tunanin irin na su na son kai.

Yayin taron, wani dan jarida ya tambayi dalilin da ya sa kasar Sin ta ba da tallafi kudi da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 32 don gina babban hedkwatar kungiyar raya tattalin arzikin yammacin Afirka ta ECOWAS.

Da yake amsa tambayar, Lu Kang ya bayyana kungiyar ECOWAS a matsayin muhimmiyar kungiya ta wata shiyyar nahiyar Afirka, wadda ta ba da gudunmowa sosai ga kokarin wanzar da zaman lafiya da dunkulewar tattalin arziki a yammacin Afirka. Kuma Kasar Sin ta dade tana taimakawa kunigyar ECOWAS wajen samun karin karfi, ta yadda za ta kara taka muhimmiyar rawa a fannonin tabbatar da zaman lafiya da ciyar da tattalin arziki gaba a yammacin Afirka gami da daukacin nahiyar Afirka. Ya ce yadda kasar Sin ke tallafawa kungiyar ECOWAS, wani bangare ne na aikin kasar na taimakawa nahiyar Afirka, domin ta kara samun ci gaba da hadin kai, gami da zaman lafiya.

Jami'in ya kara da cewa, yadda ake fama da koma bayan kayayyakin more rayuwa, shi ne dalilin da ya hana nahiyar Afirka samu karin ci gaba. Kana a nata bangare, kasar Sin ta dauki nauyin gina ofishin kungiyar ECOWAS ne bisa bukatar hakan da kungiyar ta yi. Ya ce Jita-jitar da aka yada game da wannan aiki tamkar kallon kasar Sin ne bisa tunanin kansu na son kai. Sai dai Jami'in ya tabbatar da cewa, jita-jitar ba za ta girgiza huldar hadin kai dake tsakanin Sin da Afirka ba, kuma babu wanda zai iya hana Sin da Afirka samun ci gaba a tare. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China