in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikici ya barke tsakanin jami'an tsaron Libya da wasu 'yan bindiga a yammacin Libya
2018-02-22 10:16:50 cri
Rikici ya barke tsakanin jami'an tsaron kasar Libya da wasu 'yan bindiga a garin Al-Maya mai nisan kilomita 30 daga yammacin Tripoli babban birnin kasar.

Wani jami'i daga cikin jam'an tsaron ya ce Rikicin ya barke ne tun da tsakar ranar jiya Laraba a garin Al-Maya, bayan wasu dakaru na musammam sun kai samame tungar wasu bata gari dake sacewa da kashe mutane.

Jami'in ya ce 'yan bindigar sun rufe wani bankin kasuwaci ta hanyar bude wuta, inda suka yi amfani da shi wajen kai hari.

Ya ce bayan dakarun na musammam sun cafke wasu daga cikin 'yan bindigar tare da kashe wasu, ciki har da shugabansu, sai daruruwan 'yan bindigar suka fito daga yankunan dake kusa don kai wa 'yan uwansu dauki.

Jami'in ya ce za a ci gaba da ba-ta kashin har sai an kame dukkan 'yan bindigar, ya na mai cewa dukkan wani yunkuri na shiga tsakani dan ganin mayakan sun ajiye makamai tare da mika wuya cikin ruwan sanyi, ya ci tura.

Jami'in dai bai bayyana yawan asarar rayuka da aka yi yayin rikicin ba. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China